Godiya ga Sukuk; a kalla hanyoyi 71 dake sassa daban daban na kasar nan, zasu amfana da shirin gina su, koma gyara ga wasu, yayin da shirin zaiyi kokarin samar da gadoji 4 domin saukaka sufurin tafiye tafiye, dakon kaya, dama habakar lamurran kasuwanci da zai bunkasar da tattalin arziki.
Ministar kudi, kasafi dama tsare tsare ta kasa Hajiya Zainab Shamsuna Ahmad, ta sanar da ware zunzutun kudi har naira biliyan Daya da Naira Miliyan Talatin (N130bn) domin aikin gina hanyoyi a sassa shida na kasar nan ciki kuwa harda birnin tarayya Abuja.
Hukumomin da aka damkawa kudaden domin aiwatar da ayukkan sune: maaikatar ayukka da gidaje ta kasa dama hukumar kula da birnin tarayya Abuja.
A cewar ministar ma’aikatun zasu raba kudaden ne domin soma aiwatar da ayukkan Gina hanyoyin da kuma gyara ga wasu.
Sai dai Zainab din tace tanadin fitar da kudin na kunshe ne a daftarin kasafin kudin 2022, Wanda majalissar dokoki ta kasa tace amincewa da kasafin zai kasance ne a watan Maris Mai zuwa.